Oxford ta sa kalmomin Okada, Damfo, Mama Put, dsr a cikin kamus
Fitaccen Kamus din Duniya, Oxford, sun sa kalmonin Najeriya 29 a cikin sababbin kalmomin Ingilishin da aka kirkiro a wannan shekarar.
Mafi yawan kalmomin da aka kirkiro sun shahara ne a Najeriya, wanda wasunsu aka sansu a Najeriya tun a shekarun 1970 zuwa 1980.
Babban Editan Kamus din na Oxford, Danica Salazar, ta bayyana wannan cigaba da aka samu a wani jawabi da ta fitar inji Jaridar Guardian.
Daga cikin kalmomin da aka kara a kamus din Ingilishi akwai ‘Nexr Tomorrow’ watau Jibi. Sauran kalmomin sun hada da ‘Okada’ da ‘Danfo’.
Ga jerin kalmomin da aka kirkiro:
KU KARANTA: Barawo ya yi batar dabo yayin da 'Yan Sanda ke bincike
Agric
Barbing salon
Buka
Bukateria
Chop
Chop-chop
Danfo
Flag-off
Kannywood
K-leg
Mama Put
Next tomorrow
Non-indigene
Gist
Guber
Okada
Put to bed
Rub minds
Send forth
Sef
Severally
Tokunbo
Zone
Zoning
Kannywood ce ‘Yar auta daga cikin kalmomin da aka kirkiro. Tun shekaru 50 da su ka wuce ake amfani da ‘Next Tomorrow’ a kasashen Duniya.
‘Buka,’ da ‘Bukateria’, 'Tokunbo', 'Sef', 'Guber', 'Gist' da kalmar ‘severally’ sun zama kalmomin da ke cikin kawannan mus da ake ji da shi a Duniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng