Siyasar 2019 ta raba kan Jama’a sosai a Jihar Sokoto Inji Sarkin Musulmi
A Ranar Talata ne Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya koka da yadda zaben bara ya jawo rabuwar kai da sabani har cikin ‘Yanuwa.
Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa zaben ya yi sanadiyyar da ta sa aka samu rabuwar kai a tsakanin dangi da sauran ‘yanuwa a jihar Sokoto.
“Ba a taba yin lokaci a tarihin jihar mu ba da sabanin siyasa ta kusa yi mana illa irin wannan (2019) da yanzu kotun koli ta warwarewar matsalar” inji Sultan.
Mai alfarman ya yi wannan bayani ne a lokacin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya kai masa ziyara a fadarsa a Ranar Talata, 20 ga Watan Junairun 2020.
Mai girma gwamnan ya yarda cewa siyasar 2019 ta jawo gaba tsakanin ‘Dan uwa da ‘Dan nuwa da kuma Makwabata da Abokan arziki, wanda hakan bai dace ba.
KU KARANTA: 2019: Tunani na za a karbe mani kujera ta a kotun koli - Bala
Sarkin Musulmin kasar ya nuna akwai bukatar a samu hadin-kai a jihar kamar yadda aka san Sokoto a tarihi. “Mu daina yi wa siyasa kallon a mutu ko ayi rai.”
“Mu daina tunanin cewa kowa sai ya samu abin da ya ke so. Mulki na Allah. Duk wanda ya samu, ya nuna halin girma, wanda ya rasa kuma ka da ya matsa.”
Abubakar ya yi kira ga Gwamna Aminu Tambuwal ya yi amfani da nasarar da ya samu wajen jawo kowa a jika tare da gargadin PDP game da shiga giyar-mulki.
A na sa jawabin, Tambuwal ya sha alwashin bada muhimmanci game da harkar ilmi, kiwon lafiya da canza tunanin jama’a da kawo cigaba a jihar Sokoto.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng