Sojoji sun kama masu amfani da kakin soji wajen garkuwa da mutane a Kaduna (Hoto)

Sojoji sun kama masu amfani da kakin soji wajen garkuwa da mutane a Kaduna (Hoto)

Wata rundunar sojojin ruwa ta kama wasu masu laifi da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi kauyukan karamar hukumar Kachia da sauran sassan jihar Kaduna.

Kazalika, rundunar ta kubutar da mutane 28 da masu garkuwa da mutane ke tsare da su tare da mika su ga iyalansu.

Da yake jawabi yayin mika masu laifin ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a ranar Juma'a, kwamandan rundunar sojojin ruwan, Rear Admiral Tanko Yakubu, ya ce sun samu nasarar kama 'yan ta'addar ne bayan shafe kusan watanni hudu suna bibiya da farautar masu laifi da suka addabi Kachia da sauran sassan jihar Kaduna.

"A wurare daban - daban muka kama su bayan mun kammala samun dukkan wasu bayanan sirri a kansu."

Sojoji sun kama masu amfani da kakin soji wajen garkuwa da mutane a Kaduna (Hoto)
Sojoji sun kama masu amfani da kakin soji wajen garkuwa da mutane a Kaduna
Asali: Twitter

"Mun kama wasu daga cikinsu a cikin surkukin jeji inda suke buya, yayin da wasu muka kama su a Otal, wasu kuma a gidansu."

DUBA WANNAN: Akwai shingen tsare ababen hawa na 'yan Boko Haram a kan hanyar zuwa Maiduguri - Rundunar soji

"Masu laifin da muka kama sune ke aikata miyagun laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, satar shanu, da sauransu," a cewarsa.

Ya kara da cewa sun samu makamai, babura, kakin sojoji da sauran wasu kayan laifi a wurin masu laifin da suka kama.

Masu laifin da aka kama sun hada da; Abubakar Duguri wanda aka fi sani da Kure, Saleh Magaji wanda aka fi sani da Bodori, Idris Iliyasu, Auwal Yahaya, Monore Abu, Mohammed Wakili, Tanimu Ibrahim wanda aka fi sani da Sambo, Abdullahi Adamu wanda aka fi sani da Yellow da kuma Umar Alhassan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel