Adhama zai cigaba da ba Buhari shawara game da sha’anin Matasa da Dalibai

Adhama zai cigaba da ba Buhari shawara game da sha’anin Matasa da Dalibai

A makon da ya gabata mu ka samu labari cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wanda zai rika ba shi shawarwari kan harkar Matasa.

Kamar yadda rahotanni su ka zo mana, Nasir S. Adhama ne ya koma kan kujerarsa na Mai taimakawa shugaban Najeriya a kan sha’anin Matasa.

A 2015 shugaban kasan ya fara nada Nasir Adhama a kan wannan kujera, inda ya shafe shekaru hudu a ofis, zuwa Watan Mayun shekarar bara 2019.

Malam Nasir Adhama ya sake yin dace wannan karo, inda shugaban Najeryar ya sake dauko shi domin ya cigaba da rike wannan muhimmiyar kujera.

A lokacin da ya ke rike da kujerar Hadimin shugaban kasa a wancan karo, Adhama ya yi kokarin kirkiro tsarin P-Yes domin ganin Matasa sun samu aiki.

KU KARANTA: Wata Ministar Shugaba Buhari ta ba 'Diyarta mukami a ofishinta

Adhama zai cigaba da ba Buhari shawara game da sha’anin Matasa da Dalibai
Nasir Adhama ya koma ofishinsa na Mai ba shugaban kasa shawara
Asali: Twitter

Ana sa ran cewa wannan shiri zai dawo da karfinsa a yanzu inda za a dauki akalla Matasa 100, 000 da za a koya masu aiki a wasu jihohi 12 da ke fadin kasar.

Adhama gogaggen ‘Dan siyasa ne, wanda kafin a nada shi Mai bada shawara, ya taka rawar gani wajen tafiyar shugaba Muhammadu Buhari tun 2002.

Malam Adhama ya yi takarar kujerar majalisar dokokin Kano a karkashin jam’iyyar CPC a 2011. Haka zalika ya rike mukamai masu yawa a tafiyar siyasar.

Wanan bawan Allah da ya fito daga jihar Kano ya na cikin kwamitin Matasa na majalisar dinkin Duniya watau UN. Yanzu jama’a su na ta masa fatan alheri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel