TNN: An taso Fayemi a gaba na cewa APC za ta iya rushewa bayan Shugaba Buhari

TNN: An taso Fayemi a gaba na cewa APC za ta iya rushewa bayan Shugaba Buhari

Gwmanan jihar Ekiti. Kayode Fayemi, ya na fuskantar suka a wajen wani Yanki na Kudu maso Yammacin Najeriya, a dalilin kalaman da ya yi kwanan nan.

Dr. Kayode Fayemi ya fito ya na cewa jam’iyyar APC mai mulki za ta iya rugujewa bayan saukan shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan kujerar mulki.

Wannan magana sam ba ta yi wa wasu ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki dadi ba. Daga ciki akwai Yaran fitaccen Jagoran APC a Kudu maso Yammacin kasar.

Kunle Okunola, wani shugaban kungiyar TNN masu yi wa Bola Tinubu harin shugaban kasa, ya fito ya yi magana, inda ya ce Fayemi ya na neman bata ruwa ne.

A cewar Kunle Okunola, bai kamata ‘Yan jam’iyya su damu da kalaman gwamnan ba. Okunola ya nuna cewa APC za ta cigaba da mulki ko bayan shugaba Buhari.

KU KARANTA: An fara ziga Atiku ya sake fitowa takarar Shugaban kasa a 2023

TNN: An taso Fayemi a gaba na cewa APC za ta iya rushewa bayan Shugaba Buhari
Gwamna Kayode Fayemi ya na ganin APC za ta rushe idan ba ta gyara takun ta ba
Asali: Depositphotos

A na sa ra’ayin, Okunola ya na ganin babu wanda ya cancanta da rike Najeriya bayan shugaba Buhari sai Bola Ahmed Tinubu, kuma ya na sa ran za ayi hakan.

“Duk mai maganar wargajewar tafiya, ya zama ‘Dan bata-ruwa. Ya na amfana daga jam’iyyar. A ra’ayi na, ka da wanda ya damu kansa da kalaman Fayemi.”

“Ina tunanin ayi watsi da duk wani Mai hangen rushewar jam’iyya. Wadannan mutane su na tunani ne bisa la’akari da abin da za su samu da kuma son ransu.”

TNN ta na kokarin ganin tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu ya samu mulkin Najeriya a 2023. Wasu na ganin cewa mulki zai koma Kudancin Najeriya a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel