2023: Za a yi rikici idan arewa ta kafe a kan sake yin takarar shugaban kasa - Dattijan kudu

2023: Za a yi rikici idan arewa ta kafe a kan sake yin takarar shugaban kasa - Dattijan kudu

Gabannin zaben Shugaban kasa na 2023, dattawan Kudu maso Kudu sun bayyana cewa za a yi rikici da ka iya tarwatsa kasar idan har arewa ta ce lallai zai ta cigaba da rikon shugabancin kasar bayan karewar wa’adin mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dattawan Kudu maso Kudun sun bayyana cewa ya kasance adalci barin yankin ta samar da Shugaban kasa na wasu shekaru kuma domin ta cike wa’adinta na biyu.

Da yake jawabi a wani hira a karshen mako a Abuja, Shugaban kungiyar dattawan kudu maso kudu, mai martaba, Anabs Sara Igbe ya bayyana cewa yankin ce mafi dacewa da shugabancin kasa a 2023 a kudu.

Ya yi jayayyar cewa ba lallai ne arewa ta so marawa dan kudu maso gabas baya ba a yanzu saboda yakin basasa inda aka kashe Igbo da ama, inda ya kara da cewa har yanzu Ndigbo na fama da radadin zargin mayar dasu saniyar ware.

Ya kuma yi ikirarin cewa arewa ba za ta marawa kudu maso yamma baya ba duba daga matsayar Miyetti Allah kan kayan tsaro da yankin ta kaddamar a kwanan nan.

Sara Igbe, wanda ya kuma kasance babban sakataren labaran kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF), ya bayyana cewa Kudu maso Kudu ce daidai a kasar kuma za ta bari kudu maso gabas ta ji kamar baa manta da ita ba.

KU KARANTA KUMA: Dattawan Bauchi sun roki jama’a da su amince da hukuncin kotun koli ba tare da rigima ba

Ya kuma yi ikirarin cewa kudu maso gabas na fafutukar neman kasar Biyafara sannan kuma cewa tana da muradin sake fasalin lamuran kasar amma ba wai shugabancin 2023 ba haka ma kudu maso yamma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel