Zanga-zangar da PDP za su shirya ba zai yi wani armashi ba – Timi Frank

Zanga-zangar da PDP za su shirya ba zai yi wani armashi ba – Timi Frank

Timi Frank ya yi magana a game da shirin da ‘Ya ‘yan PDP su ke yi na gudanar da zanga-zanga a game da hukuncin da kotun koli ta yi a game da zaben gwamnan jihar Imo.

Kwamred Timi Frank ya bayyana cewa wannan yunkuri na ‘Yan adawar ba zai yi wani abin kwarai ba. Tsohon Jigon na APC ya bayyana wannan ne a jiya Ranar Asabar.

Frank wand aa baya ya na cikin shugabannin APC mai mulki, a na sa hasashen ya na ganin zanga-zangar da PDP za ta shirya ba zai ko ina ba, a na sa ganin ma, an makara.

A cewar Frank, PDP ta makara wajen shirya zanga-zangar domin kuwa ba ta yi zanga-zanga a lokacin da aka tsige Walter Onnoghen daga kan kujerar Alkalin Alkalai ba.

Haka zalika Frank ya na ganin jam’iyyar hamayyar ta yi sake a lokacin da kotun koli ta yi watsi da karar Atiku Abubakar na zaben 2019, amma ‘Ya ‘yan PDP su ka yi gum.

KU KARANTA: Buhari ya sa baki game da hukuncin da aka yi wa wani Malamin Najeriya a Saudi

Zanga-zangar da PDP za su shirya ba zai yi wani armashi ba – Timi Frank
Zanga-zanga: An bar gini tun ranar zane – Frank
Asali: Depositphotos

Bayan haka, tsohon Mataimakin Mai magana da yawun jam’iyyar APC, ya kuma zargi manyan PDP kamar Gwamnoni, da yi wa babbar jam’iyyar hammayar zagon kasa.

Bayan gwamnonin Ribas da Benuwai Nyesom Wike da Samuel Ortom, ‘Dan siyasar na Bayelsa ya zargi duk gwamnonin PDP da neman kamun kafa wajen shugaban kasa.

‘Dan adawar ya ce wasu gwamnonin adawar, su kan nemi alfarama a fadar shugaban kasa, har ya soki Okezie Ikpeazu wanda yanzu su ka tafi kasar waje da shugaba Buhari.

Timi Frank ya zargi gwamnoni 14 na PDP da hada-kai da APC wajen karya jam’iyyarsu cikin sauki. Wannan ya sa jam’iyyar ta gaza aikinta a matsayin Mai adawa inji sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel