Daga bangaren Kudu maso Yamma za a fito da wanda zai zama Shugaba – Inje Awe

Daga bangaren Kudu maso Yamma za a fito da wanda zai zama Shugaba – Inje Awe

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar Ekiti, Jide Awe, ya bayyana cewa mutanen Kudu maso Yammacin Najeriya ne za su fito da shugaban kasan da za ayi nan gaba.

Kamar yadda rahotanni su ka iso mana, Cif Jide Awe ya yi wannan bayani ne lokacin da aka gayyace sa zuwa wani gidan rediyo na Voice FM mai lamba 89.9 a Ekiti.

Babban ‘Dan siyasar ya yi magana game da siyasar 2023, Dakarun Amotekun da aka kirkiro a yankin Kudancin kasa, tare da sukar kalaman kungiyar Miyettti-Allah.

Jagoran jam’iyyar ta APC ya ce shugaban kasan da za ayi a 2023, zai fito ne daga Kudu maso Yamma, saboda tsarin kama-karya da aka saba aiki da shi a Najeriya.

Awe ya kuma nuna cewa ba siyasa ta sa aka kafa jami’an tsaron Amotekun ba, tare da cewa ko ma dai ya aka kare, dole mutanen Kudu maso Yamma za su karbi mulki.

KU KARANTA: Ministan ‘Yan Sanda ba ya goyon bayan Gwamnonin Yarbawa a kan Amotekun

Game da kalaman kungiyar Miyettti-Allah, Awe ya ce: “Sun ce ba za su ba mu mulki a 2023 idan gwamnonin jihohi su ka hakikance a kan tsare jama’ansu ba.

“To, ba kungiyar ta ke bada mulki ba. Su kuma sani cewa mulki a hannun Yarbawa zai fada a 2023. Mun taka ta mu rawar ganin, idan dai maganar APC ake yi.”

Cif Awe ya kuma jinjinawa gwamnonin jihohin Kudu maso Yammacin kasar da su ka kafa jami’an tsaronsu domin tsare rayuka da dukiyoyin wadanda ke yankin.

Jigon na APC a kasar, ya kuma soki soki matsayar gwamnatin tarayya inda ya ce ba za su zura idanu ana kashe jama’a, gwamnatin tarayya ba ta yi komai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel