Ba za mu yarda a sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba - Minista Dingyadi

Ba za mu yarda a sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba - Minista Dingyadi

Mai girma Ministan harkokin ‘Yan Sandan Najeriya, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, ya fito ya yi maganar farko a game da Dakarun da aka kirkira na Amotekun.

Muhammdu Maigari Dingyadi ya nuna alamun ba ya goyon bayan gwamnonin Kudu maso Yammacin Najeriya da su ke kokarin shawo kan matsalar rashin tsaronsu.

Alhaji Maigari Dingyadi ya gargadi masu wannan aiki da cewa su bi a hankali da dokar kasa. Ministan ya ja kunnen gwamnonin ne game da sabawa kundin tsarin mulki.

Ministan ya bayyana cewa sha’anin tsaro ya rataya ne a kan wuyan gwamnatin tarayya, kuma babu wanda ya ke da hurumin aron bakin ta da nufin ci mata albasa kan wannan.

Mai girma Ministan harkokin ‘Yan Sandan ya yi wannan jawabi ne a Garin Sokoto a lokacin da ya yi magana da ‘Yan jarida game da Dakarun Amotekun da aka kafa a kasar.

KU KARANTA: Amotekun: Yarbawa sun fadawa Buhari ya ja kunnen Ministan shari'a

Maigari Dingyadi ya fadawa Manema labarai cewa sun yaba da kokarin gwamnoni kan inganta tsaro a jihohinsu, amma kuma ba za su bari wannan ya wuce gona da iri ba.

Har ila yau Daily Trust ta rahoto Ministan ya na cewa: “Kundin tsarin mulki ya fayyace komai a kan wannan (batun tsaro), kuma ba za mu bari a bi ta kan dokar kasa ba.

A jawabin na sa, Ministan ya yi magana game da shirin da ake yi na janye Sojoji daga wuraren da aka yi galaba a kan ‘Yan ta’adda, ya ce za a kai Dakarun ‘Yan Sanda wurin.

Dingyadi ya nuna cewa a shirye ‘Yan Sanda su ke da su kare rayuka da dukiyoyin jama’a a wadannan wurare. Da zarar an gama komai, za a janye Sojoji, a aika ‘Yan Sanda.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel