Masoyan Gwamna Tambuwal da Ganduje sun rungumi addu’a saboda zaman kotu
Magoya bayan gwamnan jihar Sokoto watau Aminu Waziri Tambuwal, da na Abokin hamayyarsa Ahmed Aliyu sun shiga faman addu’o’i saboda shari’ar zaben gwamnan jihar.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa haka wannan yanayi ya ke a jihar Kano, inda Magoya bayan Abdullahi Umar Ganduje su ke ta addu’a domin ganin kotun koli ta ba APC gaskiya a shari’a.
A farkon makon nan ne ake sa ran Alkalan babban kotun Najeriya za su bayyana wanda ya ke da gaskiya a karar shari’a zaben gwamnan jihar Kano da Sokoto da aka yi a farkon shekarar 2019.
“Mu na ta addu’o’i na musamman game da shari’ar. Mu na neman taimakon Allah duk lokacin da aka shiga hali irin wannan, abin da mu ke yi kenan.” Inji wani Masoyin Gwamnan Sokoto.
Sakataren jam’iyyar PDP na Sokoto, Kabir Aliyu ya ce: “Mu na sa ran samun nasara a wurinmu, domin babu abin da zai canza. Alkalai za su tabbatar da zabin jama’a da hukuncin sauran kotu.”
KU KARANTA: Ana neman karbe wasu Jihohin mu a kotun koli - PDP
A daidai wannan lokaci, ita ma jam’iyyar APC ta dage da irin wannan zaman addu’o’i a Sokoto. Sambo Bello Danchadi ya shaidawa ‘Yan jarida cewa APC ta na rokon nasara wajen Ubangiji.
A jihar Kano, kotun Allah-ya-isan ta sa Masoyan gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC sun fara shirya addu’o’in sa-kai da nufin Ubanigiji ya sake ba jam’iyyar APC nasara a shari’ar zaben.
Magoya bayan Injiniya Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida sun nuna cewa sun fara hango nasara tun bayan abin da ya faru a a kotun koli a karar zaben gwamnan jihar Imo.
Wadanda su ke tare da Abdullahi Ganduje sun zargi PDP ta furofanda inda su ka ce har a kotun koli, APC ce za ta sake samun nasara. PDP a na ta bangaren, ta yi kira ga jama’a su bi doka.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng