Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro

Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro

- Sa'o'i kadan kafin jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi zuwa birin London, ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro

- Har yanzu dai ba a tabbatar da cewa ko taron da suka saba yi ne ko kuma na gaggawa bane ya samu

- Taron ya zo ne bayan kwanaki 17 da suka yi wani taro a fadar shugaban kasar dake Aso Rock

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri da shugabannin tsaro a fadarsa dake Aso Rock a Abuja. An gano cewa ya shiga taron da shugabannin tsaron ne ana sauran sa'o'i kadan ya daga zuwa birnin London.

Rahoton ya nuna cewa, akwai yuwuwar taron ya zama daya daga cikin tarukan da yake yi da shugabannin tsaron kasar nan, inda suke bayyana mishi halin da kasar ke ciki ta fuskar tsaro.

Legit.ng ta gano cewa ana wannan taron ne bayan kwanaki 17 da suka yi makamancinsa a fadar shugaban kasar dake Abuja.

DUBA WANNAN: Hotunan ziyarar da Ahmed Musa da 'yan kungiyarsa suka kai wa yariman Saudiyya

Taron shugabanniin tsaron da aka yi a watan Disamba anyi shi ne don yin bayani ga shugaban kasar a kan halin da tsaron kasar ke ciki, kuma shugabannin tsaron sun hada da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu.

Shugabannin tsaron sun samu jagorancin ministan tsaro ne, Manjo Janar Bashir Magashi. Shugabannin sojin da suka samu halartar taron sun hada da Janar Abayomi Olonisakin, Air Marshal Sadique Abubakar, Ibok Ekwe Ibas.

Idan ba zamu manta ba, Ali Ndume, sanata

daga jihar Borno ne ya bada dalilan da suka sa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki sauya shugabannin tsaro. Ndume, shugaban kwamitin soji a majalisar dattijai ya sanar da hakan ne a wata hira da aka yi dashi da jaridar This Day.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel