Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Shugaban DSS a Benue

Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Shugaban DSS a Benue

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wani tsohon Shugaban rundunar tsaro ta farin kaya a jihar Benue, Peter Unogwu.

An tattaro cewa wanda aka sacen, wanda ke gudanar da otel din four-star a Igunale, hedkwatar karamar hukumar Ado da ke jihar, na a kan hanyar Otukpo-utonkon-Igumale lokacin da masu garkuwa da mutanen suka farma motarsa sannan suka dauke shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Wata majiya ta bayyana a kan wayar tarho cewa an sace tsohon shugaban tsaron na Chevron Nigeria Limited a wajen aikin siminti na Igumale da ke karamar hukumar Ado na jihar a hanyarsa ta dawowa daga Otukpo zuwa Igumale d misalin karfe 5:00 na ranar Laraba.

Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su sanya baki cikin lamarin rashin tsaro da ke addabar al’umman Igumale, cewa hedkwatar karamar hukumar ya zama mai hatsari gare su yayinda garkuwa da mutane ya zama ruwan dare.

Hakan na zuwa ne kasa da wata guda bayan an sace wani babban dan kasuwa wanda ya fito daga yankin sannan masu garkuwa dashi suka sa aka biya miliyoyin naira kafin su sake shi.

Sai dai kuma, a daidai lokacin kawo wannan rahoton masu garkuwa da mutanen basu bude kafar tattaunawa da iyalan mutumin ba.

An tattaro cewa Wannan shine karo na uku da irin haka ke faruwa cikin watanni shida a yankin Igumale na jihar.

KU KARANTA KUMA: Safarar yara: 'Yan sanda sun kama Farfesa a Kano

Da aka tuntube shi, jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, DSP Catherine Anene ta tabbatar da lamarin cewa a yanzu yan sanda na bibiyar masu garkuwan.

“Anyi garkuwa da tsohon shugaban na DSS a jiya. Yanzu haka jami’anmu na bibiyar masu garkuwan,” in ji ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel