Buhari ya daukarwa matan Najeriya manyan alkawara 2 yayinda ya kaddamar da sabuwar ma’aikatar harkokin mata

Buhari ya daukarwa matan Najeriya manyan alkawara 2 yayinda ya kaddamar da sabuwar ma’aikatar harkokin mata

Shakka babu shekarar 2020 zai kasance daya daga cikin shekaru mafi kyau ga mata a tarihin Najeriya yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ma’aikatar harkokin mata a Abuja a ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na gyara tattalin arziki da jin dadin jama’a domin habbaka tattalin arziki a fadin kasar.

Daga cikin alkawaran da Shugaban kasar ya yi a Abuja a ranar Alhamis yayin bikin kaddamar da ginin ma’aikatar, harda na inganta ilimin yara mata a Najeriya.

Kan haka, Shugaban kasar ya ce: “musamman, muna mayar da hankali sosai kan ilimin yara mata. Yawan yadda mata ke barin makarata ko rashin kammala karatunsu abun damuwa be sosai sannan kuma ya zama dole a magance shi.”

Sannan kuma Shugaban kasar ya ba yan Najeriya mata tabbacin cewa zamanin yiwa yara mata auren wuri ya kau a karkashin gwamnatinsa.

KU KARANTA KUMA: Hukuncin kotun koli: Buba Galadima ya yi hasashen abunda ka iya zama makomar Ganduje

Shugaban kasar ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar za ta kula da duk wani abu da ya shafi mata ta hanyar hada kai da gwamnatocin jiha da kungiyoyin kasa da kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng