Bulama: NWC ta na tare da Oshiomhole game da zabinsa na Sakataren Jam’iyya - Eta

Bulama: NWC ta na tare da Oshiomhole game da zabinsa na Sakataren Jam’iyya - Eta

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Kudancin Najeriya, Hilliard Eta, ya yi fatali da zargin Takwaransa, Mustapha Salihu.

Hilliard Eta ya karyata zargin da Jagoran APC na bangaren Arewa maso Gabas ya yi na cewa za a kakaba Waziri Bulama ne a kan kujera.

Mista Eta ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi magana da wasu ‘Yan jarida a wayar tarho a Ranar Laraba, 15 ga Watan Junairu, 2020.

Da ya ke magana game da abin da Salihu ya ke fada, sai ya ce, ‘Ba gaskiya ba ne.” Eta ya ce Mutanen Arewa maso Gabas su ka zo da batun.

“Shugaban jam’iyya ya jagoranci zaman da aka yi, da aka zo kan maganar Sakataren jam’iyya, duk mun yarda cewa a nada Waziri Bulama.”

KU KARANTA: Atiku ya ba tsohon Gwamnan Imo shawara ya rungumi kaddara

Bulama: NWC ta na tare da Oshiomhole game da zabinsa na Sakataren Jam’iyya - Eta
Eta ya ce NWC ta yi na'am da matakin da Oshiomhole ya dauka
Asali: UGC

Eta ya bayyana abin da ya faru da cewa: “Shi mataimakin shugaban jam’iyya na Arewa maso Gabas bai so haka ba, abin da ya faru kenan.”

“Nada sabon Mukaddashin Sakataren jam’iyya ya samu karbuwa ne daga majalsar NWC bayan shawarar da mu ka karba daga ‘Ya ‘yan APC.”

“Dole ka bar wa mutanen Arewa maso Gabas siyasar Arewa maso Gabas. Su su ka hadu a kan cewa mu nada Waziri Bulama.” Inji Hilliard Eta.

Jagoran jam’iyyar ya bayyana cewa an ba Mustapha Salihu watanni shida ya fito da sabon Sakataren jam’iyya bayan tafiyar Mala Buni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel