Damfara: Kotu ta daure Mutumin Najeriya da Budurwarsa da laifi a Ingila
Rahotanni daga gidan watsa labarai na TWNews sun bayyana cewa an kama wani Mutumin Najeriya da aikata mugun laifi a Birtaniya.
A Ranar Juma’ar da ta wuce, aka damke Oluwaseun Ajayi da wata Baiwar Allah mai suna Inga Irbe da ake tunanin cewa Mai dakinsa ce.
Binciken da aka yi ya nuna cewa Oluwaseun Ajayi da Inga Irbe sun kware wajen damfarar Bayin Allah su na samun kazaman kudi a Ingila.
A dalilin haka ne Alkalin wani karamin kotu da ke Birtaniya ya yankewa mutanen biyu hukuncin dauri a gidan Maza tare da aikin wahala.
Ajayi zai shafe shekaru biyar da aikin wahala na shekara guda, yayin da Macen za ta yi watanni shida a gidan yari da aikin akalla sa’a 170.
KU KARANTA: Gaskiyar binciken da ake yi wa Shehu Sani - Hadiminsa
Mista Ajayi mai shekaru 39 da Irbe ‘Yar shekara 49 su na zaune ne a titin Orchard da ke Unguwar Dagenham da ke Gabashin Birnin Landan.
Kotu ta samu wadannan mutane da laifin damfara ne a Nuwamban 2019. Ajayi da Irbe sun yi wa asusun bankin mutane akalla 770 kutse.
Daga cikin laifuffukan da aka kama Ajayi da su, har da kin bayyana lambar sirrin wayar salularsa domin gudan bankado barnar da ya ke yi.
Da aka yi bincike a gidansu, an samu wayoyin salula da su ka hada da iPhone, Huawei, Nokia da wasu layin waya da gafaka da dai sauransu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng