Isa Ali Pantami ya fadawa Gwamnoni su janye karin farashin RoW
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi kira ga jihohin da su ka yi karin farashinsu na RoW da ake biya da su janye wannan mataki da su ka dauka.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin kafafen zamani, Isa Ibrahim Pantami, ya ce wannan karin da aka yi zai dawo ya shafi Talakawan gari.
A wani jawabi da Ministan kasar ya fitar a Ranar Talata, 14 ga Watan Junairu, 2020, ya koka da jihohin da su ka tada farashinsu na RoW.
A cewar Ministan, an taba kafa wani kwamiti a 2013 wanda ya amince da N145 a matsayin farashin RoW a kan kowane mita da aka ja.
Mai girma Ministan ya ce matakin da wasu gwamnonin jihohi su ka dauka a yanzu ya ci karo da matsayar majalisar tattalin arziki na NEC.
KU KARANTA: Ministan sadarwa zai yi maganin cogen 'Data' a Najeriya

Asali: Twitter
RoW shi ne kudin da gwamnonin jihohi su ke karba daga kamfanonin Najeriya da su ka ja layin sadarwa da ya ratsa ta karkashin kasarsu.
“Abin takaici ne mu ji cewa wasu jihohi sun yi watsi da wannan matsaya, a wasu jihohin an yi karin kudin RoW na fiye da kashi 1, 200%.”
“Wannan zai kawowa kokarin da gwamnatin tarayya ta ke yi tasgaro. Akwai alaka mai karfi tsakanin karfin sadarwa da alkaluman GDP.”
Dr. Pantami ya kuma kare da cewa wannan kari zai shafi gudanarwar kamfanonin, wanda a karshe nauyin zai dawo kan sauran jama’a.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng