Hadimi: Akwai gaurayen siyasa a binciken da EFCC ta ke yi wa Shehu Sani

Hadimi: Akwai gaurayen siyasa a binciken da EFCC ta ke yi wa Shehu Sani

Suleiman Ahmed, wanda ya na cikin Hadiman tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Shehu Sani, ya fayyace shari’ar da ake yi tsakanin Mai gidan na sa da hukumar EFCC a wata hira.

Ahmed ya ce Shehu Sani ya fara haduwa da Sani Dauda ne bayan da ya samu sabani da wani Surukinsa har aka tsare sa, a dalilin haka Sanatan ya je gida domin ya yi masa jajen lamarin.

Wajen wannan ziyara ne shugaban kamfanin na ASD Motors ya yi wa Sani tallar wata mota. A karshe Sani Dauda ya yi masa alfarma ya biya kudin motar gutsun-gutsun inji Hadiminsa.

“Wata rana ya kai masa ziyara a ofis a Kaduna ya ba shi $13000, daga baya ya kara masa $11000. Daga nan ya ba shi takardar shaida da lambar banki domin ya tura ragowar kudin motar.”

A game da shiga hannun EFCC, Ahmed ya ce a Ranar karshe ta 2019 EFCC ta gayyaci Sanatan ya zo ofishinta, kuma ya je salin-alin, a nan aka soma zarginsa da cewa Dauda ya ba shi wasu kudi.

KU KARANTA: Ba ni da wata alaka da Sanata Shehu Sani Inji CJN

Hadimi: Akwai gaurayen siyasa a binciken da EFCC ta ke yi wa Shehu Sani
Shehu Sani ya soki mulkin APC daf da za a damke shi kwanan nan
Asali: UGC

Sanata Sani ya yi wa EFCC bayani cewa shi ne ya ba ‘Dan kasuwar kudi ba wai akasin haka da nufin ya ba Ibrahim Magu cin hanci ba. Wannan ya sa EFCC ta tsare shi kafin ya samu beli.

A cewar Hadimin ‘Dan siyasar, bayan Shehu Sani ya yi ido-biyu da Dauda, ‘Dan kasuwar ya fada masa cewa wani Yaronsa ne ya rubuta korafi a kansa, domin shi bai iya karatu ko rubuta ba.

Alhaji Dauda ya kuma ce ya yi magana da Isa Funtua wani Aminin shugaban kasa, inda ya shaida masa cewa ‘Dansa ya yi kuskuren maka Shehu Sani gaban EFCC, don haka ya sa baki a cece sa.

Suleiman Ahmed ya ce daga baya ne jami’an su ka canza baki su ka ce ‘Dan siyasar ya nemi ba Alkalin Alkalai cin hanci. Ya ce sukar gwamnatin Buhari ta sa aka taso Mai gidan na sa a gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel