Masari ya baiwa masu garkuwa sa’o’i 48 su saki mutanen da suka sace ko su fuskanci fushin sa

Masari ya baiwa masu garkuwa sa’o’i 48 su saki mutanen da suka sace ko su fuskanci fushin sa

Gwamnatin jahar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari tare da hadin gwiwar rundunar Sojan kasa sun baiwa yan bindiga wa’adin sa’ao’i 48 su sako duk mutanen dake hannunsu ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Daily Trust ta ruwaito Masari ya bayyana haka ne bayan wata ganawar sirri da ya yi da wasu tubabbun yan bindiga a jahar Katsina, tare da wakilan yan bindigan da suka ki amsan tsarin sulhu da zaman lafiya, a fadar gwamnatin Katsina.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An garkame fadar gwamnatin jahar Imo bayan hukuncin kotun koli daya tsige gwamnan

Bayan kammala ganawar, sakataren gwamnatin jahar, Alhaji Mustapha Inuwa ya bayyana cewa: “Abin ya isa haka, mun fada musu wannan shi ne zaman sulhu na karshe da za mu yi dasu, kodai su rungumi zaman lafiya ko kuma sojoji su kutsa kai cikin dazukan su kai musu farmaki.

“Mun kuma gargade su da cewa duk wasu mutanen da suke rike dasu a yankin Jibia, Batsari da sauran yankunan su gaggauta sakin su zuwa ranar Alhamis, idan kuma ba haka ba komai ta fanjama fanjam! Saboda ba zamu bari wasu yan tsiraru da basu rungumi zaman lafiya su kawo mana matsala ba.

“Mun ji dadin goyon bayan da muke samu daga wadanda suka rungumi tsarin zaman lafiyan suke bamu, ta hanyar hada kai da gwamnati da jami’an tsaro wajen ganin an samar da zaman lafiya a yankin Safana, Danmusa da sauran yankunan kudancin jahar.” Inji shi.

Idan za’a tuna a makon da ta gabata dakarun rundunar Sojan kasa sun gudanar da wani gagarumin samame a mafakar miyagu yan bindiga a jahar Katsina, inda suka kashe yan bindiga da dama da aka kiyatsa yawansu ya haura 100, tare da kubutar da wadanda aka sace da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel