Sunaye: An rantsar da alƙalan kotun Shari'a a Abuja

Sunaye: An rantsar da alƙalan kotun Shari'a a Abuja

Babban alkalin tarayya, Ishaq Bello, ya rantsar da sabbin alkalai uku na kotun daukaka karar shari'ar musuulunci. Bello, wanda shine shugaban kwamitin shari'a na tarayya, yayi kira ga sabbin alkalan da su tabbatar da adalci ba tare da tsoro ba.

Sabbin alkalan sune Surajo Mohammed, Abubakar Mahmoud da Hassan Aliyu.

Yayi kira garesu da su tabbatar da adalci a fannin shari'a ta hanyar yin abinda ya dace da tanadin addinin musulunci.

"Dole ne ku kasance masu mutunta nagartar kanku da ta cibiyar da kuke wakilta" in ji shi.

Bello ya cigaba da jan kunnensu a kan su kiyaye duk wata mu'amala tasu da kuma abinda zasu furta ballantana a cikin mutane.

Ya kara da ce musu su kasance masu kara nazari a kan littafan addini kuma su karkade kunnuwansu daga kafafen yada labarai. "Ku dage tare da jajircewa don cimma abinda kuka yi niyya. Idan aka zo bincike, hatta alkalin alkalai ba zai kama ku da laifi ba matukar kunyi abinda ya dace" cewar sa.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace hakimi a Kano

A yayin zantawa a kan kalubalen da ke gabansu, Muhammed, wanda yayi jawabin a madadinsu, yace "a matsayin majistare da na rike na shekaru hudu, na san kalubalen dake ciki da wajen wannan aikin. Amma in har mutum yayi niyyar yin adalci, babu wani abinda zai rinjayi hukuncinsa."

"Karbar rashawa, kowacce iri ce abin tsoro ne a kowanne lokaci. In har alkali ya shirya yin aiki nagari, toh ba zai saka kansa a cikin rashawa ba. Matukar aka fara karbar rashawa, tana lalata aiki da sauri fiye da kiftawar ido." cewar Muhammed.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel