Kotun koli ta saka sabuwar rana domin yanke hukunci a kan kujerar Tambuwa

Kotun koli ta saka sabuwar rana domin yanke hukunci a kan kujerar Tambuwa

Kotun koli ta kasa, a karkashin alkalin alkalai na kasa, Jastis Mohammed Tanko, ta tsayar da ranar 20 ga watan Janairu domin yanke hukunci a kan karar kalubalantar kujerar gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

A wani hukuncin da ta zartar a yammacin ranar Talata, 14 ga watan Janairu, kotun kolin ta kwace kujerar gwamnan Imo, Emeka Ihedioha, dan jam'iyyar PDP tare da tabbatar da Hope Uzodinma, dan jam'iyyar APC a matsayin halastaccen zababben gwamnan jihar.

Kotun, mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkakalai na kasa (CJN), Mohammed Tanko, ta ce ba Ihedioha ne halastaccen zababben gwamnan jihar Imo ba.

Babbar kotun, wacce ake wa lakabi da 'daga ke sai Allah ya isa', ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) data karbe shahadar cin zabe daga hannun Ihedioha tare da mika shi ga Uzodinma ba tare da wani bata lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng