Fasinjojin mota sun yi wa Faston karya jini-da-majina a Garin Onitsha

Fasinjojin mota sun yi wa Faston karya jini-da-majina a Garin Onitsha

Mun samu labari cewa wani mai wa’azi ya ga ta kansa a tashar motar nan ta Upper Iweka da ke cikin Garin Onitsha a jihar Anambra.

Wani Bawan Allah da ya ke yi wa jama’a wa’azi a motar haya su tuba, ya samu matsala da jama’a bayan an gan shi dauke da bororon roba.

Bororon roban sun fado ne daga cikin littafin Injila da ya ke amfani da shi wajen wa’azi kamar yadda ake rade-radi a jaridar Vanguard.

Bayan jama’a sun ga faduwar wadannan abubuwa daga littafin Mai wa’azin ne su ka fito da shi daga mota, su ka yi masa mugun duka.

Uche Chukwujekwu wanda aka yi komai a gaban idonsa, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa mutumin ya je ne ya na yi wa jama’a addu’o'i.

KU KARANTA: Za a hana auran matan da ba su kammala karatu ba a Kano

“Wa’azi ya kai wa’azi daga bakin wannan mai karyar Malanta, ya na bada tabarruki, har wasu Fasinjoji sun mika wuya ga Yesu.”

“Abin sha’awa, ya bude Injilarsa domin karbar sadakar da wasu Fasinjoji su ka ba shi, kwatsam sai ga bororon rabo 3 sun fado.”

“Nan sai Mutanen da su ka fusata da Faston da sauran masu fakewa su na bara daga cikin motar su ka fito su ka fara yi masa duka.”

Mista Chukwujekwu ya ce a nan Malamin karyat ya shiga rusawa jama’a ihu ayi masa rai domin ta haka ne ya ke samun na abinci.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu Jami’an ‘Yan Sanda ne su ka ceci wannan Malami yayin da ake ba shi ‘dan karen kashi a cikin tasha.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel