Jama’a za su yi cincirindo wajen daukar Malaman Makaranta a Legas

Jama’a za su yi cincirindo wajen daukar Malaman Makaranta a Legas

Suru Avoseh, wanda ya na cikin hukumar da ke kula da ma’aikatan gwamnati a jihar Legas, ya yi magana game da Malaman makaranta da za su dauka.

A Ranar 12 ga Watan Junairu, 2020, Avoseh ya bayyana cewa fiye da 50, 000 mutum su ka nuna sha’awar yin aikin koyarwa a makarantun gwamnatin jihar.

A cewar Avoseh, mutane 1, 000 za a dauka wannan aiki domin su zama Malaman makaranta. Za a bi matakai kafin a zakulo sababbin Malaman makarantan.

“Bayan an yi jarrabawa, za a gayyaci wadanda su ka yi kokari domin su zo ayi masu jarrabawar baki-da-baki ta intabiyu” A haka ne za a fitar da gwanaye.

KU KARANTA: Jamilu Gwamna ya dauki karatun wasu Matasa a kasar waje

“Yanzu haka mun fara aika sakonni ta layin wayar salula ga wadanda su ka yi nasara a jarrabawar.” Avoseh ya bayyana wannan wajen wani taro.

"Ta tabbata ba kaf wadanda su ka nemi aikin za a dauka ba, kuma ba duk wadanda su ka ci jarrabawa za su zama Malamai ba." Inji jami’in gwamnatin.

Mista Suru Avoseh ya kuma bayyanawa Manema labarai cewa ba da dadewa ba hukumar SUBEB da hukumar kula da ma’aikata za ta raba wadannan ayyuka.

Ya ce, sai bayan an tantance wadanda za a dauka ne sannan hukuma za ta sanar da Mai girma gwamna Babajide Sanwo-Olu adadin sababbin ma’aikatan jihar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel