Yusaku Maezawa ya na neman Budurwar da za ta bi shi Duniyar wata

Yusaku Maezawa ya na neman Budurwar da za ta bi shi Duniyar wata

Yusaku Maezawa, wanda ya na cikin manyan masu kudin da ke kasar Japan, ya na neman Budurwar da zai zagaya Duniyar wata da ita.

Kamar yadda mu ka samu labari, Mai kudin ya na neman wata sabuwar Budurwa da za su ci Duniyarsu a tsinke bayan ya rabu da Budurwarsa.

Kafin yanzu Yusaku Maezawa ya na tare ne da wata Tauraruwar wasan kwaikwayo. A halin yanzu ya zama allura cikin ruwa da mai rabo ke dauka.

Attajirin ya sa an soma yi masa tallar neman Masoyiya wanda ta haura shekaru 20. Ana haska tallar a kafafen gidan talabijin Japan kai tsaye.

Mai kudin ya na son wanda za ta yi soyayya da shi, ta bi shi zuwa wata domin ya wartsake daga kadaicin gwaurantakar da ta ke damunsa.

KU KARANTA: Rikici ya kaure tsakanin Gwamnan Kaduna da Yusufu

Yusaku Maezawa ya na neman Budurwar da za ta bi shi Duniyar wata
Maezawa ya na so ya taka wata a kumbon Space X a 2023
Asali: Facebook

“Yanzu shekara ta 44. Yayin da kadaici da kewa ya soma lullube ni a hankali, abu daya na ke tunani; soyayya da mace guda.” Inji Maezawa.

Maezawa ya kuma shaidawa kowa a wanna talla cewa ya na neman wanda za su zagaya Duniyar wata tare. Me zai hana mu zuwa Duniyar wata?

A Ranar 17 ga Watan Junairun 2020, za a fitar da sunayen wadanda su ka yi nasarar tsallake matakin farko na zaben Budurwar Attajirin.

A Watan Maris mai kudin zai zabi wanda ta kwanta masa a rai. Maezawa shi ne Mai kamfanin nan na Zozo wanda aka saidawa Yahoo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel