Bafarawa: Rigimar Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II za ta iya shafar kaf Arewacin Najeriya

Bafarawa: Rigimar Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II za ta iya shafar kaf Arewacin Najeriya

Mun samu labari cewa tsohon gwamnan Sokoto wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 watau Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya yi magana game da rikicin Kano.

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ja kunnen mahukunta da cewa abin da ya ke faruwa a jihar Kano, zai iya yin naso ga sauran Masarautun da ke Arewacin kasar.

Attahiru Bafarawa ya nuna cewa a na sa ra’ayin ba ya goyon bayan faskara masarautar Kano da aka yi, wanda hakan ya na iya jawo siyasa ta bata gidan sarauta.

Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi wata hira da gidan VOA na Amurka a Ranar Alhamis, 9 ga Watan Junairu, 2020.

Alhaji Bafarawa ya na ganin cewa babu wanda ya ke da laifi a wannan rikici irin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin shi ne Uban ‘Yan kasa gaba daya.

KU KARANTA: Gwamnati ta na zargin Sarkin Kano Sanusi II da wata badakala

Bafarawa: Rigimar Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi II za ta shafi kaf Arewacin Najeriya
Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ce bai kamata a taba masarautar Kano ba
Asali: Depositphotos

Duk Arewacin Najeriya babu wanda jama’a su ke jin maganarsa sai Muhammadu Buhari, don haka Bafarawa ya ke ganin ya kamata ace shugaban ya sa bakinsa.

Bafarawa wanda ya yi ikirarin cewa shi ne ya fara kokawa game da abin da ya ke faruwa a Kano watanni takwas baya, ya ce shugaban kasa ya dace ya shiga lamarin.

A na sa shawarar, abin da ya kamata ayi shi ne shugaba Buhari ya zauna da Sarkin Kano da Mai girma Gwamna domin ayi sulhu, ba wai a kafa wani kwamiti ba.

Wannan mataki da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka na barka masarautar Kano zuwa gida biyar ya sa an shigo da siyasa cikin sarauta inji ‘Dan siyasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel