Mahaifina ya mutu ina shekara 8, amma ban gaji kudinsa ba - Inji Dangote

Mahaifina ya mutu ina shekara 8, amma ban gaji kudinsa ba - Inji Dangote

Attajirin Najeriya Alhaji Aliko Dangote ya bayyana yadda ya mallaki makudan kudi ha rake jin sunansa a ko ina a fadin Duniya.

Aliko Dangote ya bayyana wannan ne lokacin da ya yi hira da David Rubenstein na Bloomberg Africa a makon da ya gabata.

Attajirin ya tabbatar da cewa ya tashi a gidan arziki domin Kakan kakansa, Alhassan Dantata ya taba zama Mai kudin Afrika.

Dangote ya kuma bayyana cewa Kakan Mahaifinsa, Alhaji Sanusi Dantata, ya na cikin masu kudin da aka yi a zamaninsa.

Alhaji Dangote wanda shi ne na 96 a cikin jerin masu kudin Duniya, ya ba kowa mamaki da ya ce bai gaji dukiyar Mahaifinsa ba.

Mai kudin ya ce Mahaifinsa wanda ya kasance ‘Dan kasuwa kuma ‘Dan siyasa ya mutu ne yayin da shi ya ke shekaru 8 rak a Duniya.

Mahaifi na ya mutu ina shekara 8, amma ban gaji kudinsa ba - Dangote
Dangote ya ce dagewa ya yi da nema a maimakon cin kudin Mahaifinsa
Asali: UGC

KU KARANTA: Wasu manyan Darektocin Dangote sun ajiye aiki a kamfaninsa

A wannan hirar ta ‘Dangote da ta fito kwanan nan, ya bayyana cewa fadi tashi ya yi ta yi a rayuwa har ya samu ya kai inda ya kai.

“Na fara harkar kasuwanci ne a 1978, ina sayo kaya in saida. A shekarar 1980 na fara shigo da sukari da shinkafa da sauran kaya.”

“A 2003 na fara gina kamfanin siminti, wanda na kammala a 2007. A lokacin ton miliyan 1.8 ake samu a Najeriya. Mu ka fara da 5.”

A game da abin da ya sa ya fi ba siminti karfi, Dangote ya nuna cewa akwai matsalar rashin gidaje da abubuwan more rayuwa a Najeriya.

A dalilin haka ne ‘Dan kasuwan ya yi fice yanzu a kasashe da-dama na Sahara har ya zama Attajirin da duk Afrika babu irinsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel