‘Dan kwadago ne ni Inji wanda aka kama da lambar Hannan Buhari

‘Dan kwadago ne ni Inji wanda aka kama da lambar Hannan Buhari

An samu bayanai game da wani Bawan Allah da ake zargin cewa an same shi ya na amfani da wani layin waya na ‘Diyar shugaban kasa, ya na aikata ta’adi.

Bayanai sun fito game da labarin wannan mutumi da jami’an tsaro su ka cafke sa. Kamar yadda mu ka samu labari, ainihin sunansa shi ne Mista Okolie Anthony.

Okolie Anthony ya bayyana cewa kwadago ya ke yi na aikin gini ya na samun kudi. Kafin nan ya ce ya taba zama dilallin caca amma ya hakura da sana’ar daga baya.

Mista Anthony yanzu haka ya na kiwon kifi ne ya na samun kudi tare da wani Mutumi a gidansa da ke cikin Kauyen Oktuogwu a Garin Asaba da ke jihar Delta.

Wannan mutumi ya ce ya samu wannan layin waya mai dauke da sunan Hannan Buhari ne a wajen mutumin da ya ke kiwo a gidansa, bayan shi ya sayi layin a titi.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna ya ce ba zai taba bari a saki El-Zakzaky ba

‘Dan kwadago ne ni Inji wanda aka kama da lambar Hannan Buhari
Jami'an tsaro sun kama wanda ya ke amfani da tsohon layin wayar Hannan Buhari
Asali: Facebook

Okolie ya nuna cewa ya yi mamaki bayan ya fahimci cewa lambar wayarsa ta 09035666662 ta na nuna sunan ‘Diyar shugaban kasa da zarar an bincika a waya.

Jaridar Vanguard ta ce Okolie Anthony ya samu kan sa a matsala ne bayan da ya rika amfani da wannan lambar waya ya na yaudar mutane da sunan Hannan.

“A Ranar 21 ga Watan Yulin 2019, aka kama ni bayan na yi amfani da layin na aikawa wani sako ina neman taimakon kudi, kuma ya yi alkawarin zai ba ni.”

“Ban sake yi masa magana ba, domin ban san wanene shi ba, ba.” Okoli ya shaida wannan da bakinsa. A karshe ya karyata cewa ya nemi ya kashe kansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: