Daurin aure ya hada El-Rufai, Kwankwaso, Sule a Garin Zariya

Daurin aure ya hada El-Rufai, Kwankwaso, Sule a Garin Zariya

A jiya Ranar Asabar, 11 ga Watan Junairun 2020, aka daura auren ‘Diyar wani fittacen ‘Dan kasuwa a Garin Zariya, Alhaji Kabiru Dauda.

Kamar yadda mu ka samu labari, tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan ‘Yan siyasa sun halarci daurin auren.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya na cikin wadanda su ka samu halartar wannan daurin aure da aka yi a Unguwar Kongo.

Bayan nan Kwankwaso ya halarci daurin auren Khadija Abbas Lawal da Ramadan Nuhu Danburam wanda Iyayensu manyan 'Yan siyasa ne.

Haka zalika rahotanni sun nuna cewa ba a bar Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Mal. Nasir El-Rufai, da Jama’ansa a baya wajen wannan taro ba.

KU KARANTA: Atiku, Tinubu, Osinbajo sun halarci auren gidan Nuhu Ribadu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramalan Yero, Dallatu Zazzau ya na cikin wadanda su ka shaida wannan daurin aure a jiya.

Sauran ‘Ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki da su ka halarci taron sun hada da Arch. Bala Bentex wanda ya rike mataimakin gwamnan jihar a 2015.

Sauran ‘Yan jam’iyyar PDP wanda daga ciki har da wani jigo a majalisar amintattu na jam’iyyar sun samu halartar wannan daurin aure da aka yi.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ne ya tsayawa Amarya Bilkisu Kabir Dauda a matsayin Waliyyi, ya kuma karbi sadakinta a nan ta ke.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel