'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar dan majalisar Jigawa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar dan majalisar Jigawa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Haruna Dangyatum, dan majalisa jihar Jigawa mai wakiltar mazabar Miga. Abdu Jinjiri, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya ce 'yan bindiga uku ne suka yi awon gaba da Zahra'u Haruna a ranar Asabar wajen karfe 4 na asuba a kauyen Dangyatum da ke karamar hukumar Jahun ta jihar Jigawa.

"A yau ne wajen karfe 4 na asuba wasu 'yan bindiga suka tsinkayi kauyen Dangyatum da ke karamar hukumar Miga da ke jihar Jigawa, inda suka yi awon gaba da Zahra'u Haruna, matar dan majalisa mai wakiltar mazabar," Jinjiri yace.

"Yan bindiga uku ne suka isa har gidan dauke da bindigogi da adda kuma suka yi awon gaba da ita zuwa inda har yanzu ba a sani ba. Amma a halin yanzu 'yan sanda suna kan matsalar don shawo kanta." ya kara da cewa.

A ranar Asabar da ta gabata ne wasu wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne suka harbe Anyinu tare da sace matarsa da diyarsa a yankin Abaji da ke birnin tarayya na Abuja.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umurnin gina gidaje 1,000 a jihar Borno

Lamarin ya auku ne kauyen Nuku dake kan babban titin Rubochi a sa'o'in farko na ranar Asabar.

A jihar Bayelsa kuwa, an sace diyar kwamishinan ruwa, Nengi Talbota, mai shekaru 6 a duniya a watan Disamba na 2019.

'Yan bindigar har su hudu sun tsinkayi gidan kwamishinan wajen karfe 11:30 na dare tare da yin gaba da Antonio mai shekaru shida kacal a duniya. Amma kuma, rundunar 'yan sandan jihar sun yi nasarar ceto ta a ranar Laraba da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel