Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana makomar El-Zakzaky

Kwamishinar shari'a ta jihar Kaduna, Mai shari'a Aisha Dikko, ta ce makomar shugaban kungiyar musulmai mabiya akidar shi'a, Malam Ibrahim El-Zakzaky ta dogara ne a hannun kotu.

Kwamishinar ta sanar da hakan a ne wata takarda da ta fitar a ranar Alhamis, ta ce gwamnatin jihar Kaduna bata da nufin janye zargin da take mishi, amma ta bar kotu ta yanke hukunci.

Ta ja kunnen cewa wannan shari'ar kada ta zamo wani abu da za a yi kamfen a kafafen yada labarai ko kuma wajen tursasawa kowacce iri.

A cigaba da bayanin dalilin da yasa gwamnatin jihar ba za ta saki shugaban IMN din ba, Dikko ta jaddada cewa El-Zakzaky da matarsa Zeenat na fuskantar zargi ne na laifuka takwas, wadanda suka hada da kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne.

DUBA WANNAN: Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba muddin ina shugaban ƙasa - Trump

Idan kuwa za a tuna, kotu ta hana bukatar belin da wadanda ake zargin suka mika tun a watan Augsuta 2018.

Ta ce: "A zaman karshen da kotu tayi a ranar 5 ga watan Disamba 2019, an dage sauraron shari'ar zuwa 6 ga watan Fabrairu 2020 tare da umarnin adana su a gidan gyaran hali kafin a cigaba da shari'ar. Babbar kotun ce take da alhakin bada makomarsa kuma dokar kassar ta tanadi mutunta kotu har zuwa lokacin da za a kammala shari'ar."

Kwamishinar shari'ar ta ja kunnen kafofin yada labarai da ke ikirarin cewa wasu jami'ai za su daga da Zakzaky zuwa New Delhi ba tare da jiran hukuncin kotu ba don gano ingancin lafiyar ma'auratan. Ta ce kowa ya koyi darasi daga abinda ya faru a birnin na New Delhi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel