Kano: Shugabannin Kananan Hukumomi na PDP sun sauke Rabiu Bichi
shugabannin kananun hukomi, sun hadu sun ruguza kaf shugabannin jam’iyyar PDP 27 na jihar Kano da ke karkashin Rabiu Sulaiman Bichi.
Shugabannin da ke rike da jam’iyyar adawar a kananan hukumomi 44 na jihar Kano ne su ka sanar da ‘Yan jarida wannan a Ranar Laraba.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Daily Trust, Mahammina Bako Lamido, ne aka nada a matsayin shugaban rikon kwarya na PDP.
Mahammina Bako Lamido ya dare kan kujerar ne kamar yadda ya bayyana a Sakariyar jam’iyyar bayan an tsige majalisar Injiniya Rabiu Bichi.
A cewar sabon shugaban jam’iyyar da aka kafa, dokar PDP ce ta bada damar a sauke shugabannin rikon kwaryar da ke kan kujerar a baya.
KU KARANTA: 2019: Magudi aka tafka a zaben Kano Inji Rabiu Kwankwaso

Asali: Twitter
Alhaji Bako Lamido ya ce sashe na 31 (2) (e) na kundin tsarin mulkin PDP ya ba shugabannin rikon kwarya wa’adin watanni uku ne rak.
Bako Lamido ya ce sun sanar da hedikwatar jam’iyya da ke Abuja game da cikar wa’adin shugabannin da ke rike da jam’iyyar tun bara.
Duk da cewa shugabannin kananan hukumomi sun aikawa uwar jam’iyya takarda a 2019, ba a dauki matakin kauda su daga mukamansu ba.
Wannan ya sa wadannan jagorori na jam’iyyar hamayyar su ka ruguza shugabannin da aka kafa bayan dawowar Rabiu Musa Kwankwaso PDP.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng