Tirka tirkan IPPIS: Kungiyar malaman jami’a ta yi ganawar sirri da shugaban Buhari a Villa

Tirka tirkan IPPIS: Kungiyar malaman jami’a ta yi ganawar sirri da shugaban Buhari a Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga wata ganawar sirri da shuwagabannin kungiyar Malaman jami’a, watau ASUU, inda ake sa ran tattaunawarsu za ta tattara ne game da batun sabon tsarin biyan albashi na bai daya, watau IPPIS.

Idan za’a tuna, ASUU sun yi fatali da wannan sabon tsarin biyan albashi, inda suka bayyana cewa tsarin zai gurgunta ayyukan malamai a jami’o’in Najeriya tare da kawo tsaiko ga tsarin koya da koyarwa.

KU KARANTA: Kaico! Yaro dan shekara 14 ya mika kan sa ga masu garkuwa da mutane a Kaduna

Daily Trust ta ruwaito shi dai wannan tsari na IPPIS gwamnati ta kirkiro shi ne da nufin rage rashawa, satar dukiyar jama’a, saukaka samun da biyan albashi da kuma toshe duk wasu ramuka da kudaden gwamnati ke sulalewa.

Sai dai a lokacin da malaman wasu jami’o’i suka amsa kiran gwamnati wajen shiga tsarin, wasu malaman kuma basu yarda an gudanar da aikin a makarantunsu ba saboda matsayin hawa dokin na ki da ASUU ta yi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su shiga wannan tsari na IPPIS wanda ke karkashin ofishin babban akanta na kasa da sa idon ministan kudi. Hatta jami’an Soji da Yansanda sun shiga cikin wannan tsari.

A wani labarin kuma, guda daga cikin dattawan Arewa, kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar Switzerland, Yahaya Kwande ya bayyana cewa duk ya kai shekara 90 a rayuwa, ba zai mutu ba har sai ya ga Atiku Abubakar ya zama shugaban kasar Najeriya.

Kwande ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi, inda yace a yanzu babu mutumin da Najeriya yake tsananin bukata ya jagoranceta a siyasance a matsayin shugaban kasa kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abunakar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel