Bincike ya nuna 'Yan Kenya da Najeriya sun fi kaunar Trump

Bincike ya nuna 'Yan Kenya da Najeriya sun fi kaunar Trump

Wani rahoto daga cibiyar bincike ta Pew Research Centre ya nuna cewa mutanen kasashen Kenya da Najeriya na sahun gaba wajen kauna da aminta da lamuran Shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

Cibiyar ta gudanar da wani kuri’a don jin ra’ayin jama’a game da yadda jama’a suka dauki shugaba Trump.

Kuri'ar ta gano cewa kaso 65 na al’umman kasar Kenya da aka ji ra'ayinsu suna matukar kaunar Trump tare da aminta da al'amuransa, inda kaso 58 na mutanen Najeriya su ma suka kasance masu kaunarsa.

Mutanen kasashen biyu dai na kaunar Trump duk da irin abubuwan rashin jin dadi da ya yi wa 'yan Afirka a baya kamar bayyana Afirka da 'masai'.

Kasashen guda biyu na Afirka dai na cikin kasashe 33 da aka gudanar da binciken a wajen Amurka a tsakanin watan Mayu da Oktoban 2019.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ta’adanci zai cigaba a arewa maso gabas – Ndume

Nazarin na Pew ya kuma nuna cewa yankin kasashen Afirka yamma da hamada na nuna gamsuwa da Amurka.

A wani labari na daban, mun ji cewa ‘Yan Majalisar Wakilan tarayyan kasar Amurka sun nuna cewa ba za su bari shugaban kasa Donald Trump ya tafi yaki da Iran ba.

Jam’iyyar hamayya ta Democrat wanda ta fi rinjaye a majalisar wakilai ta bayyana cewa za ta kada kuri’ar rashin goyon bayan yaki.

Kakakin majalisar Amurka, Nancy Pelosi, ta ce ‘Yan jam’iyyarta a majalisa za su dauki mataki domin ganin kasar ba ta jawo yaki ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel