Bode George ya girgiza Yaran Bola Tinubu da shirin takarar Shugaban kasa

Bode George ya girgiza Yaran Bola Tinubu da shirin takarar Shugaban kasa

Rahotanni su na zuwa mana cewa Yaran siyasar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun shiga wani yanayi na dar-dar a cikin ‘yan kwankin nan.

Kamar yadda rahotanni su ke zuwa, kaddamar da shirin takarar Bode George a 2023, shi ne abin da ya fara rikirkita mutanen Bola Tinubu.

Cif Bode George wanda ya na cikin manyan jam’iyyar PDP mai adawa, ya nuna cewa zai nemi takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Wannan yunkuri na Bode George, ya na iya jawowa Asiwaju Bola Tinubu matsala ganin cewa duk sun fito ne daga Garin Legas a Yankin Kudu.

Ko da Bola Tinubu bai fito ya ce zai yi takara a 2023 ba, alamu sun nuna cewa Magoya bayansa su na shiryen-shiryen ganin ya gaji Buhari.

KU KARANTA: Yaran Tinubu sun fara wasu kulle-kulle domin karbe Majalisa

Bode George ya girgiza Yaran Bola Tinubu da shirin takarar Shugaban kasa
Cif Olabode George zai fito takarar Shugaban kasa a 2023
Asali: UGC

Masoyan tsohon gwamnan na Legas sun yi mamakin jin labarin cewa George ya na harin kujerar shugaban kasa, wanda wannan ya taba su.

Daily Trust daga wata Majiyar APC ta bayyana cewa wasu na-hannun daman Tinubu su na ganin ‘Dan adawar ba zai kawo masu cikas ba.

“Bode George ba abin tsoro ba ne. George ya girmi Tinubu, ya lashe zaben Legas a baya, kuma har gobe (Tinubu) ya ke cin zabe a Legas."

“Don haka Tinubu ne babban ‘Dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya a 2023.” Inji wani Yaron Tinubu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel