Umar Kabir: Gangaran da ya yi nasara wajen Musabaqar kasa ta 34

Umar Kabir: Gangaran da ya yi nasara wajen Musabaqar kasa ta 34

A gasar Al’-Kur’ani mai girma da aka yi na wannan karo, wani Bawan Allah mai suna Umar Kabir, ne ya zo na farko a kaf Najeriya.

Alaranma Umar Kabir, ‘Dan ainihin jihar Kaduna ne, kuma yanzu haka ‘Dalibi ne a jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke cikin Garin Zariya.

Kamar yadda mu ka samu labari daga wani Bawan Allah, Kabir, ya na karantar ilmin fasaha ne a wannan fitacciyar jami’ar ta tarayya.

Umar Kabir ya samu nasara ne a gasar da aka yi a Legas wanda cibiyar Musabaka da Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto su ka shirya.

Kabir ya haddace littafi mai tsarki na Al-Kur’ani da kuma tajwidinsa. Wannan ya sa ya samu jinjina daga ko ina a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Kasar Iran ta kai wa Dakarun Amurka hari a sansanin Iraki

Mai martaba Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, shi ne ya karrama wannan Bajimin Alaranma wanda ya yi zarra.

Daga cikin kyautar da ya samu akwai sabuwar mota fil kirar Nissan Almera. Bayan haka kuma an ba shi makudan kudi a matsayin kyauta.

A rukunin mata kuma, Diya’atu Sanni, wanda ta fito daga jihar Kano ce ta yi nasara a bangaren manyan mahaddatan Al-Kur’ani na bara.

Wannan ne karo na 34 da aka shirya babbar musabakar Al-Kur’ani inda duk wani Mahaddaci da ake ji da shi a fadin kasar ya ke gwabzawa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel