Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban jigon APC a Ondo
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), James Ajulo a jihar Ondo.
Ajulo ya kasance shugaban jam’iyyar mai mulki a Akungba-Akoko a karamar hukumar Akoko ta kudu maso yamma da ke jihar.
An tattaro cewa an sace shine a gidansa da ke Ibaka Quarters da ke garin Akungba-Akoko.
A cewar majiyoyi, yan bindigan sun far ma gidan Ajulo jim kadan bayan dawowarsa daga wata fita da ya yi sannan suka yashe gidansa kafin suka tafi da dan siyasar a motarsa.
Wani hadimin dan siyasar ya yi bayanin cewa masu garkuwan sun kai wani harin bazata kan Ajulo kafin faruwar lamarin.
A cewarsa tuni aka kai rahoton lamarin ofishin yan sandan Akungba-Akoko.
Kakakin yan sandan jihar Ondo, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin.
KU KARANTA KUMA: An kashe mutum daya yayinda magoya bayan APC da PDP suka kara a Imo
Ya bayyana cewa an fara bincike a cikin lamarin sannan an tura jami’an tsaro yankin da abun ya faru don ceto shi.
Joseph ya roki mazauna yankin da kada su tayar da hankalinsu sannan ya basu tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng