El-Rufai ya yi umurni rufe shagunan siyar da gas da ke cikin unguwanni

El-Rufai ya yi umurni rufe shagunan siyar da gas da ke cikin unguwanni

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi umurnin rufe dukkanin tashoshin siyar da gas da ke a wuraren zaman jama’a a jihar.

Gwamnan wanda ya bayar da umurnin a ranar Litinin ya roki mazauna jihar da su kai rahoton irin wadannan wurarren siyar da gas din ba tare da bata lokaci ba zuwa ga gwamnati domin daukar matakin gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa El-Rufai wanda ya ziyarci wajen da gas ya tashi a ranar Asabar a Sabon Tasha, Kaduna ya ce tashoshin gas su koma cibiyoyin kasuwanci.

Gwamnan ya shawarci jama’a da su kawo karar tashoshin gas da ke yankunan gidajen jama’a.

Ya bayyana cewa tashar gas na da hatsari sosai wanda ya kamata a dunga gudanar da harkar ne a wuraren kasuwanci inda za a iya daukar matakan kariya.

Gwamnan ya kai ziyarar jaje ga iyalan Farfesa Simon Mallam, wanda ya rasa ransa a lamarin sannan ya kuma ziyarci mutanen da lamarin ya cika da su wadanda ke jinya a babban asibtin St Gerald, Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Bam ya kashe mutane 30 a wata gada mai cike da jama’a a Borno

Ya yi addu’an jin kai ga wadanda suka mutu sannan ya yiwa wadanda ke asibiti fatan samun lafiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel