2020: Za mu fito da mutane 100m daga cikin talauci – Gwamnatin Tarayya

2020: Za mu fito da mutane 100m daga cikin talauci – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi alkawarin cewa za ta ceto mutane miliyan 100 daga talauci a wannan sabuwar shekarar ta 2020.

Kamar yadda mu ka samu labari, Ministar kudi da tattalin arziki, Zainab Ahmed Shamsuna, ce ta bayyana wannan a wata hira a jiya.

Ministar ta tsakuro hirar da ta yi da gidan talabijin na NTA wanda ta wallafa a shafinta na Tuwita a Ranar 6 ga Watan Junairu, 2020.

“Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni cewa dole mu fito da mutane miliyan 100 daga talauci, kuma wannan mu ka sa gaba.”

Bayan wannan umarni na shugaban kasa, Ministar ta ce dole a ga sauyi a Najeriya domin cin ma hakar ruwan Gwamnatin Buhari.

KU KARANTA: Jerin muhimman abubuwan da za su faru a Najeriya a shekarar bana

2020: Za mu fito da mutane 100m daga cikin talauci – Gwamnatin Tarayya
Zainab Ahmed Shamsuna ta ce Gwamnatin Tarayya za ta kawo aikin yi
Asali: Twitter

“A shekarar 2020, mu na so mu zabura sosai, domin mun fahimci cewa a irin wannan tafiyar, ba za mu kai inda Buhari ya ke mana hari ba.”

Ahmed ta ce shugaban kasar ya daura wannan nauyi ne a kan duka Ministocin kasar, don haka ne ma aka kawo wata dokar tattalin arziki.

“Za ku ga cewa kudirin da mu ka kawo ya bada karfi ne wajen saukakawa kananan kasuwanci, domin ta nan ne tattalin kasa zai motsa.”

“Saboda haka dole mu tabbatar mun samar da abubuwan yi, mun rage rashin aikin yi, mun kuma fito da ‘Yan Najeriya da-dama daga fatara.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel