Kissan Soleimani: NSCIA ta gargadi matasan Najeriya kan yin zanga-zanga

Kissan Soleimani: NSCIA ta gargadi matasan Najeriya kan yin zanga-zanga

Kwamitin koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA) a ranar Litinin ta yi kira ga matasan musulmi a Najeriya su kame kansu kan batun rasuwar babban kwamandan dakarun tsaron Iran a kasar Iraqi, Qassem Soleimani.

A sanarwar ta shugaban sashin watsa labarai na NSCIA, Ibrahim Aselemi ya fiyar a Abuja, kungiyar ta yi kira ga matasa da kada su bari zuciya ta gushe hankulansu da tunaninsu kuma su tabbatar sun kasance masu son zaman lafiya a ko da yaushe.

NSCIA ta ce matsalar da ke tsakanin Amurka da Iran kawai za a iya warware shi ne ta hanyar tattaunawa a teburin sulhu.

Sanarwar ta ce, "An janyo hankalin mu kan wata zanga-zangar lumana da wasu matasa musulmi suke shirin yi don nuna fushinsu kan kisar babban kwamandan sojojin Iran, Janar Qassem Soleimani a Iraqi.

"Duk da cewa zanga-zanga na cikin abubuwan da demokradiyya ta halasta a duk duniya, NSCIA na ganin ba wannan lokacin ya dace ayi zanga-zanga ba."

DUBA WANNAN: Neman sa'a: Duk kwana uku nake yanka wa zoben tsafi na zakara - Barawo

An kashe Mr Soleimani ne a ranar Juma'a da ta gabata sakamakon harin da Amurka ta kai a Baghadaza ta hanyar amfani da jirgi mara matuki.

Tun bayan harin da ya yi sanadiyar kisar Soleimani, kasashen Amurka da Iran suna ta musayar yawu kana lamarin ya janyo zaman dar-dar a kasashen duniya da dama kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel