Kaduna: Watakila Shugaban NAEC, Simon Mallam ya mutu a hadarin gas

Kaduna: Watakila Shugaban NAEC, Simon Mallam ya mutu a hadarin gas

Shugaban hukumar harkar da ta shafi karfin nukiliya a Najeriya NAEC watau Simon Mallam, ya na cikin wadanda ake tunanin sun rasu a wani hadari.

A cikin karshen makon nan ne gas ya yi bindiga a wata Unguwa da ake kira Sabon Tasha a Garin Kaduna, wanda wannan abu ya jawo mutuwar jama’a.

A jiya Jaridar nan ta The Cable ta samu labari cewa Simon Mallam ya na cikin wadanda hadarin ya rutsa da su a gidan Man Total da ke wannan Unguwa.

Mallam mai shekaru 64 a Duniya, shi ne shugaban hukumar NAEC, kuma ainihinsa mutumin Garin Kagoro ne a karamar hukumar Kaura a Kaduna.

Mista Mallam ya zama Farfesa ne a shekarar 2001 bayan ya dade ya na koyar da ilmin nukiliyya da sauran ilmin kimiyya a jami’ar ABU da ke Zariya.

KU KARANTA: Miyagun Makiyaya sun shiga wani Kauye sun kashe Liman da mutum 20

Kaduna: Watakila Shugaban NAEC, Simon Mallam ya mutu a hadarin gas
Ana tunanin Shugaban NAEC, Simon P Mallam ya rasu a hadarin Kaduna
Asali: Depositphotos

Tsakanin 1999 zuwa 2006, Simon Mallam ya rike mukaddashin shugaban cibiyar CERT wanda ta ke binckike da horo a kan sha’anin nukilya a Jami’ar ABU.

Wannan duk bayan irin rubuce-rubucen da shehin Malamin kimiyyar ya yi a kan fannin nukiliya wanda aka buga a manyan mukalu da ake ji da su a Duniya.

Jaridar ta ce kawo yanzu dai babu bayani da ya fito daga bakin Iyalin Farfesan, sai dai babu shakka an ji cewa ya na cikin wadanda hadarin ya aukawa.

A jawabin da Kwamishinan tsaro da harkokin gidan jihar Kaduba, Samuel Aruwan, ya fitar ba tare da kama sunaye ba, ya jajantawa wadanda musibar ta shafa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel