Jami’an Sojojin ‘Amotekun’ za su soma aiki a 9 ga Junairun 2020 – Inji Fayemi

Jami’an Sojojin ‘Amotekun’ za su soma aiki a 9 ga Junairun 2020 – Inji Fayemi

Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya sun kafa jami’an tsaronsu masu zaman kansu wanda aka yi wa suna da 'Amotekun'.

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti, ya bada sanarwar cewa wadannan jami’an tsaro za su soma aiki a cikin Watan nan.

A cewar Mai girma gwamnan na Ekiti, wadannan Dakaru za su fara aiki ne a yankin kasar a Ranar 9 ga Watan Junairu, 2019.

Dr. Kayode Fayemi ya bayyana wannan ne a jawabin murnar shiga sabuwar shekara da ya yi wa mutanen jihar Ekiti jiya Laraba.

A jawabin gwamnan na 1 ga Watan Junairun 2020, ya bayyana cewa sun kawo wannan tsari ne domin magance matsalar tsaro.

KU KARANTA: Kudu maso Yammacin Najeriya sun dauki matakin inganta tsaro

Jami’an Sojojin ‘Amotekun’ za su soma aiki a 9 ga Junairu – Inji Fayemi

Sojojin ‘Amotekun’ za su rika aiki a Ekiti, Ondo, Ogun, Legas da Oyo
Source: Twitter

Dr. Fayemi ya ce za su karfafa kokarin da sauran jami’an tsaron Najeriya su ke yi wajen samar da zaman lafiya a fadin kasar.

“A Ranar 9 ga Watan Junairu, 2020, Jami’an tsaron Kudu maso Yamma wanda ake kira Amotekun za su fara aiki a jihohi 6.”

“Ekiti ta taka rawar gani wajen wannan yunkuri wanda zai taimaka wajen kare mutanenmu da tsare jiharmu.” Inji Fayemi.

“Har gobe Ekiti ta na cikin wuraren da su ka fi ko ina zaman lafiya da mutum zai zauna ya yi aiki da kasuwanci a Najeriya.”

Sai dai, gwamnan ya nuna cewa zai yi wahala a iya kauda masu barna gaba daya daga cikin al’umma, sai dai a rage su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel