Yadda siyasar Saraki, Melaye, Shehu Sani ta gamu da cikas a zaben bana

Yadda siyasar Saraki, Melaye, Shehu Sani ta gamu da cikas a zaben bana

A Watan Yulin 2019 ne wasu ‘Yan majalisar tarayya su ka sauya-sheka daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyun hamayya. A halin yanzu Sanata guda ne daga cikinsu ya iya rike kujerarsa.

An rika samun ta-ta-bur-za tsakanin gwamnatin shugaba Buhari da majalisar Bukola Saraki. Har akwai wasu Sanatocin APC a wancan lokaci da ake ganin cewa su ne ke hana ruwa gudu.

Mun kawo jerin wasu fitattun Sanatocin da a 2019 su ka rasa kujerunsu saboda wasu dalilai:

1. Bukola Saraki

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya samu kansa a cikin sarkakiya da gwamnatin Buhari inda aka rika maka shi a kotu. A karshe dai bayan ya koma PDP, ya rasa kujerarsa a hannun Ibrahim Oloriegbe. A zaben nan ne Saraki ya rasa karfin da ya ke da shi a jihar Kwara.

KU KARANTA: Zaben da su ka ba mutanen Najeriya mamaki a shekarar 2019

2. Dino Melaye

Wani fitaccen Sanata da ake ganin ya na kawowa gwamnatin APC matsala shi ne Dino Melaye. Ko da Sanatan na Kogi ya zarce a zaben 2019, duk da ya sauya-sheka zuwa APC, daga baya kotu ta ruguza zabensa, inda daga baya ya sha kashi a hannun ‘Dan takarar APC, Smart Adeyemi.

3. Shehu Sani

Shehu Sani shi ne ya wakilci Yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan da ta shude. Ko da ya na cikin jam’iyyar APC mai mulki a lokacin, Sanata Shehu Sani ya kan fito ya soki gwamnati. Sa-in-sarsa da gwamna Nasir El-Rufai ta sa ya koma jam’iyyar PRP, amma ya sha kasa a 2019.

4. Ben Bruce

A zaben wannan shekara, Ben Murray Bruce bai nemi ya zarce a kan kujerarsa ba. Sanatan na Bayelsa shi kadai ne wanda ya fito daga Kudancin Najeriya a jerin. Murray-Bruce ya na cikin 'Yan PDP da su ka yi kaurin-suna wajen sukar gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng