'Yan sandan kasa da kasa sun cafke wani kwamishina a kan badakalar makuden kudi

'Yan sandan kasa da kasa sun cafke wani kwamishina a kan badakalar makuden kudi

Jami'an 'yan sandan kasa da kasa sun kama kwamishinan al'adu da bude ido na jihar Edo, Osaze Osemwingie-Ero a kan zaginsa da ake da badakalar wasu makuden kudade. Amma kuma gwamnatin jihar Edo din ta tsame kanta daga komai da ya shafi kama shi.

An ruwaito cewa, Osemwingie-Ero ya shiga hannun 'yan sandan kasa da kasa ne a kasar Faransa a watan Nuwamba, sakamakon kama shi da suka yi da kudi har $2m, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Jita-jita sun bayyana cewa, Gwamna Godwin Obaseki ne ya bashi makuden kudaden bayan da ya raka shi tafiya zuwa kasar ketaren.

Wata majiya kuwa cewa tayi, ana tuhumar kwamishinan ne da wani laifi da ya aikata a shekaru 7 da suka gabata.

Amma a mayar da martanin da gwamnatin jihar Edo tayi a ranar Litinin, tace wannan kamen na Osemwingie-Ero bashi da nasaba ko hadi da Gwamna Obaseki.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun tarwatsa taron 'yan Shi'a a Sokoto

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan a kan yada labarai, Crusoe Osagie yace, gwamnatin jihar bata tabbatar da wannan kamen ba.

Ya ce, "Mun gano cewa kafafen yada labarai na zamani na ta yada cewa an kama kwamsihinan al'adu da bude ido na jihar Edo, Osaze Osemwingie-Ero. Amma har yanzu gwamnatin jihar bata tabbatar da zargin kama shi din ba ko kuma dalilin da zai assasa hakan."

"Amma zamu iya tabbatarwa jama'a cewa, babu tantama, duk abinda ya kawo kamen, toh bai shafi gwamnatin jihar ba ko kuma Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo." ya kara da cewa.

Wani babban jami'i a gwamnatin jihar, wanda ya bukaci a boye sunansa yace, gwamnatin jihar ta san da kama kwamishinan, a dalilin wani laifi da ya aikata kafin ya hau kwamishinan jihar.

A kan kudi har dala miliyan biyu da aka samu a hannun kwamishinan, majiyar ta bayyana cewa bata tabbatar da hakan ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel