Ya kamata Buhari ya tsare Gwamnan CBN - Lamido

Ya kamata Buhari ya tsare Gwamnan CBN - Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari day a kama sannan ya tsare Godwin Emefiele, Gwamnan babban bankin Najeriya kan kudin makamai wanda Sambo Dasuki ya wahala a kansa.

Lamido, a shafinsa na Facebook, ya wallafa, “Kwararru biyu wadanda suka mika biyayyarsu da da’a ga Shugaban kasa.

“An umurci daya (babu mamaki kan fallen takardar kawai) da ya saki kudi ($2.3b) daga babban bankin kasar. Dayan an umurce shi da ya karbi kudin sannan ya rarraba su ga wasu jerin sunaye.

“Dukkaninsu a matsayinsu na masu biyayya kuma wadanda shugaban kasa ya nada sai suka bi umurnin da aka basu a wasikar!

“Daya ya cigaba da aikinsa sannan har yanzu yana gudanar da dukkanin umurnin da sabon ubangidansa ya bashi. Sai aka dauki dayan sanann aka gurfanar dashi a gaban kotu sannan aka yi umurnin sakinsa kan beli. Amma aka cigaba da tsare sa har tsawon shekaru hudu inda sai yanzu aka sake sa! Me yasa aka tsare shi ma tun farko?

“Ba wai yan iyalansa kawai aka tauye wa hakkin ganin jigonsu ba, Dasuki ya kasance cikin radadi da bakin cikin rasa mahaifinsa yayinda yake tsare!”

KU KARANTA KUMA: Da mugun rawa: Jirgin Arik cike da fasinja ya yi juyin gaggawa saboda wata matsala

A baya mun ji cewa Sule Lamido, ya ce sakin Sambo Dasuki da Ministan shari’a ya sa aka yi, ya nuna cewa tun farko ba zargin satar kudi ta sa aka kama shi ba.

The Guardian ta rahoto Alhaji Sule Lamido ya na cewa garkame tsohon Mai bada shawara a kan harkar tsaron bai da wata alaka da badakalar kudin makamai na Dala biliyan 2.1.

‘Dan siyasar ya fadawa ‘Yan jarida a wayar tarho cewa tsare Sambo Dasuki da aka yi, ya na da nasaba ne da sabanin da ke tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel