‘Yan Majalisa su yi waje da rokon Gwamnatin Buhari na aron $29.9 – Inji Attah

‘Yan Majalisa su yi waje da rokon Gwamnatin Buhari na aron $29.9 – Inji Attah

Fitaccen Dattijon nan kuma tsohon gwamnan Akwa Ibom, Obong Victor Attah, ya ba ‘Yan majalisar tarayya shawara ta yi watsi da rokon gwamnatin tarayya na cin bashin kudi.

A wata hira da ya yi da Jaridar Vanguard, Obong Victor Attah ya na ganin cewa idan har da dukiyar man fetur Najeriya za ta biya wannan kudi nan gaba, to gwamnati ta yi wa kanta tarko.

Tsohon gwamnan ya ba gwamnati shawarar ta fadada tattalin arzikin kasar domin a rage dogara da ma fetur, wanda a cewarsa, shi kadai ba zai iya kawowa Najeriya cigaban da ake buri ba.

Tsohon ‘dan siyasar da ya dade ya na kira ayi garambawul, ya ce: “Idan har jihohi za su rika zuwa ana kasa masu kudin da gwamnatin tarayya ta tara a wata, za su rika ganin cewa hakkinsu ne.”

“Idan har Jihohi za su zauna da kafafunsu, dole su fadada tattakin arzikinsu, su hako ma’adanan da ba a taba hakowa ba, su koma harkar noma, su bunkasa kere-kere da yawon bude idanu.”

KU KARANTA: Najeriya za tayi babban rashin idan Jamhuriyyar Nijar ta ja lantarkinta

“Kuma ba zan iya fahimtar yadda jam’iyyar da ta ke da batun yi wa Najeriya garambawul a cikin manufofinta, har ta kafa kwamiti a karkashin El-Rufai, ace ta gaza aikata abin da ta fada ba.”

“Ban ga tunanin ace yanzu mu na bukatar mu cigaba, don haka bari mu ci bashi mu kawo cigaba. Da me za ka biya bashin wannan kudi da aka aro? Da wannan kudin mai da aka ce ya yi kadan.”

“Idan na karbi aron kudi na fadada kasuwancina, alhali ina da hanyoyin samu daban-daban, wannan ya yi daidai. Amma ace da mai kurum aka dogara, wannan bai isa ya sa a ci bashi ba.”

A hirar da Victor Attah ya yi da ‘Yan jarida ya bada shawarar gwamnati ta shiga yarjejeniya da manyan kamfanonin da za su gina hanyoyi a fadin kasar, sannan su maida kudinsu daga baya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng