Masu garkuwa da mutane su na bukatar Miliyan 30 a kan Hakimin Birnin Gwari

Masu garkuwa da mutane su na bukatar Miliyan 30 a kan Hakimin Birnin Gwari

Mun samu labari cewa Miyagun da su ka sace wani Mai Gari a kasar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun bukaci Iyalinsa su biya kudi tarin kafin su sake shi.

Masu garkuwa da mutane sun sa kudi Naira miliyan 30 a kan Hakimin Birnin Gwari, Alhaji Yusuf Abubakar Yahaya, wanda ya ke hannunsu na tsawon kwanaki.

Mai martaba Hakimi da wani tsohon Jami’in harkar ilmi a jihar Kaduna, Ibrahim Musa sun shiga hannun Masu garkuwa da mutane ne a Ranar Larabar da ta gabata.

Wani Mai Gari a yankin, Imam Musa Udawa, ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa wadanda su ka yi gaba da wadannan Bayin Allah biyu, sun bukaci a ba su kudi.

KU KARANTA: 'Dan Sanda ya harbe Abokinsa, ya kuma kashe kansa da kansa

Malam Imam Udawa ya ce an bukaci a bada Naira miliyan 30 ne cir kafin a fito da Hakimin da wanda su ke tare. An sace su ne dai a kan hanyar su ta zuwa Anguwar Yako.

Udawa ya kuma fadawa Manema labarai cewa bayan dauke Hakimin da tsohon jami’in gwamnati, Masu garkuwan sun sace mutum hudu a Garin Doka kwanakin baya.

Mutane biyu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, sun dawo gida kenan bayan Iyalinsu sun biya kudin fansa Naira miliyan uku, sai kuma aka sake komawa aka sace su.

Wannan mutumi ya shaida cewa sai da Iyalin kowane daga cikin wadanda aka sace ya biya wannan makudan kudi, amma aka sadado aka sake sace su a makon jiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel