Barawon burodi, madara, kwai da man bota ya fuskanci hukuncin bulala a gaban Alkali

Barawon burodi, madara, kwai da man bota ya fuskanci hukuncin bulala a gaban Alkali

Wata babbar kotun Abuja dake zamanta a garin Zuba ya yanke hukuncin bulala goma sha biyu ga wani mutumi mai suna Yakubu Nasiru da aka kama da satar burodi, kwai da man bota.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa Alkalin kotun da ya yanke wannan hukunci, Gambo Garba ya gargadi Yakubu Nasiru daga aikata irin wannan laifi a nan gaba, sa’annan ya shawarce shi ya nemi sana’ar yi.

KU KARANTA: Da zafi zafi: Wani babban Sanatan jam'iyyar APC daga kudancin Najeriya ya rasu

Lauya mai kara, Chinedu Ogaba ya bayyana ma kotun cewa a ranar 14 ga watan Disamba ne wani mutumi mai suna Aminu Lawal mazaunin garin Dakwa ya kai kara ga ofishin Yansanda a kan cewa Yakubu ya fasa masa shago ya shiga.

Lauya Ogada ya bayyana ma kotun cewa shigar barawon keda wuya sai ya kwashe kwai, man bota da kuma manyan burodi guda uku, madarar Nono da kuma kudi N1,850 daga shagon, sa’annan ya kara da cewa an gano makamai a hannun barawon.

Sai dai wanda ake kara ya tabbatar da laifinsa ga Yansanda, sa’annna ya bayyana ma kotu cewa yunwa ce ta sanya shi shiga shagon malam Aminu domin ya samu abin da zai ci, ya kara da cewa an kama shi ne sakamakon tsayawa da yayi a shagon don soya kwan da kansa.

A wani labarin kuma, a ranar Laraba, 18 ga watan Disamba ne kotun kolin Najeriya ta hannun alkalanta ta yanke wasu hukunce hukunce a kan shari’un dake gabanta game da zaben wasu gwamnonin Najeriya daya gudana a farkon shekarar 2019.

Sai dai dayawa daga cikin gwamnonin da kararsu ta kai har gaban kotun koli sun sha, sakamakon kotun ta tabbatar da halascinsu a matsayin gwamnoni tare da yin fatali da korafe korafen abokan hamayyarsu da suka gabatar mata.

Wadannan gwamnoni sun hada da: Dapo Abiodun na jahar Ogun, Nasir Ahmad El-Rufai na jahar Kaduna, Abdullahi Sule na jahar Nassarawa, Aminu Bello Masari na jahar Katsina, Babajide Sanwo Olu na jahar Legas, Udom Emmanuel Udom na jahar Akwa Ibom, David Umahi na jahar Ebonyi da kuma Seyi Makinde na jahar Oyo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel