Daga dubbai zuwa daruruwa: Hukumar KAROTA ta zabtare yawan Adaidaita Sahu a Kano

Daga dubbai zuwa daruruwa: Hukumar KAROTA ta zabtare yawan Adaidaita Sahu a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa zata rage yawan adadin baburan adaidaita sahu da zasu dinga gudanar da sana'arsu a jihar Kano din. Zata zabtare ne daga dubu dari biyu zuwa dubu dari.

Shugaban hukumar Karota ta jihar kano din, Baffa Dan Agundi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar da sabuwar koriyar lambar masu adaidaita sahun a jiya.

Baffa Babba Dan Agundi ya kara da tabbatar da cewa, a mako mai zuwa, duk dan adaidaitan da Karota ta kama da kowanne irin hoto a jikin babur dinsa, zata cafkesa har sai ya biya kudin talla.

DUBA WANNAN: Satar kwan fitila: Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin kwanaki 21 a gidan yari

Dan Agundi ya kara shaida cewa, daga mako mai kamawa, duk wata alaka ta kungiyar direbobin adaidaita sahu da Toakan ta tarwatse, sakamkon yunkurin tada hayaniya. Kuma wannan alakar ba zata dawo ba har sai jami'an tsaro sun kammala gudanar da bincike a kan rahotan da suka mika a kan kungiyar.

Wakilan gidan rediyon Freedom, Abdulkarim Muhammad Tukuntawa, ya ruwaito cewa Baffa Dan Agundi na cewa, duk direban Adaidaita sahun da bai yi sabuwar rigistar ba har aka rufe yi a karshen wannan watan da muke ciki, Karota zata kara masa kudin tara matukar gwamnati taga damar sake bada dama ayi rigistar karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel