Zaben 2019: Ana rade-radin an gano Fowler ya karkatar da Bilyan 40 daga FIRS

Zaben 2019: Ana rade-radin an gano Fowler ya karkatar da Bilyan 40 daga FIRS

Ana kishin-kishin din cewa akwai rikici a fadar shugaban kasa game da zargin da ake yi wa tsohon shugaban hukumar FIRS, Tunde Fowler, na wawurar wasu biliyoyi a lokacin ya na ofis.

Rahotannin da mu ka samu a karshen makon nan sun ce ana zargin Mista Babatunde Fowler wanda ake maye gurbinsa da Muhammad Nami ya karkatar da kudin haraji domin harkar zabe.

A cewar PRNigeria, an yi amfani da wannan kudi ne wajen zaben wannan shekarar. Wannan ya sa aka bukaci ayi bincike domin hukunta duk wanda aka samu da laifin taba dukiyar kasar.

Abin da ya kara jagula lamarin shi ne ana zargin wani babban ‘Dan siyasar Kasar da ya fito daga yankin Kudu maso Yamma da sanun wani kaso daga cikin wannan makudin kudi har Biliyan 40.

Rahotannin sun ce wannan ‘Dan siyasa ya karbi Naira biliyan 3 ne daga cikin kudin da aka wawura. Watau shi kadai ya tashi da abin da ya haura 7% na kudin da aka karkatar daga tulun.

KU KARANTA: Shugaban APC ya yi gum da rade-radin takarar Tinubu a 2023

Majiyar ta ce jawabin da Mista Babatunde Fowler ya yi wa fadar shugaban kasa kan yadda aka kasa kudin bai gamsar da ita ba. A dalilin haka ne aka soma gudanar da bincike na musamman.

A cewar jaridar, har an damke wasu da ake zargin akwai hannunsu a wajen yin awon gaba da wannan kudi da aka tattara daga hannun ‘Yan kasa da kamfanonin da ke biyan gwamnati haraji.

“Wasu daga cikin manyan jami’an FIRS, kusan 9 daga cikinsu su na hannun hukumomin da ke yaki da satar kudin gwamnati a yanzu. Ana zargin wasunsu da hannu a badakalar kwangiloli.”

Wata Majiya daga fadar shugaban kasar ta ce: “Dadin dadawa da kuma irin almubazzarancin da wasu Hadimai da na-kusa da shugabannin hukumar FIRS su ka rika tafkawa (a lokacin).”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Online view pixel