Wani Mai saida wiwi ya nemi ‘Yan Sanda su kama masu ciniki da kudin jabu a Legas

Wani Mai saida wiwi ya nemi ‘Yan Sanda su kama masu ciniki da kudin jabu a Legas

Mun ji cewa wani Mutumi da ke saida tabar wiwi a Legas ya jefa kansa cikin matsala bayan da ya gayyaci Jami’an ‘Yan Sanda su cafke wasu mutane biyu da ke kokarin sayayya da kudin jabu.

Kamar yadda mu ka samu labari a Ranar 13 ga Watan Disamban 2019, wannan Bawan Allah da ya ke dillacin wiwi ya kai wasu mutane - Sunday Uche da Patrick Chidiebere wajen ‘Yan Sanda.

Wannan ‘Dan wiwi ya gayyaci ‘Dan Sanda ne ya kama wadannan Matasa ne bayan sun yi kokarin yin sayayya a wajen sa da wasu kudin jabu. A karshe Jami’in tsaron ya damke dukansu.

Wadannan Matasa sun yi yunkurin yi wa Mai saida tabar wiwin cinikin N21, 500, amma sai ya fahimci kudin bogi aka ba shi. Nan take ya ruga ya kira wani ‘Dan Sandan da ke aiki a lokacin.

Wannan abu ya faru ne a Ranar 3 ga Watan Disamba a kasuwar Tejuosho da ke Unguwar Yaba a jihar Legas. Yanzu an maka mutanen biyu a kotu da laifuffuka da su ka hada da rike kudin jabu.

KU KARANTA: An kama masu tada rikicin zabe a Jihohin Bayelsa da Kogi

Mai kara a gaban kotu ya ce an kama Uche da Chidiebere da takardun N1000 har 16 da N500 guda 11, Wadanda ake tuhumar sun fadawa kotu cewa ba su aikata laifuffuka da ake zargin su da su ba.

Jami’in gwamnatin ya kuma bayyanawa hukuma cewa an yi ram da wannan Dillali da laifin saida wiwi. A shari’a, amfani da tabar wiwi ya sabawa sashe na 411 da 372 na dokokin jihar Legas.

Rahotanni sun zo mana cewa Mista Sunday Uche ya na da shekaru 24 be a Duniya, yayin da shi kuma Patrick Chidiebere ya ke shekara 25 da haihuwa. Babu bayani game da Mai saida wiwin.

Za a iya daure wadannan mutane a kurkuku na tsawon shekaru biyu idan aka same su da laifi. Alkali mai shari’a E.N. Ojuromi ta daga shari’a bayan ta bada belin mutanen a kan N100, 000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel