Gwamnonin APC sun yi rikici a kan Oshiomhole wajen wani zama da Shugaban kasa

Gwamnonin APC sun yi rikici a kan Oshiomhole wajen wani zama da Shugaban kasa

Mun ji cewa Gwamnonin da ke karkashin jam’iyyar APC sun maidawa juna kalamai masu zafi, tare da yi wa ‘yanuwansu ihu a taron da aka shirya Ranar Alhamis din da ta gabata a Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa wasu daga cikin gwamnonin na APC su na neman a tsige Adams Oshiomhole daga kan kujerarsa, a daidai wannan lokaci kuma wasu su ka dage kan akasin haka.

An gaza cin ma matsaya bayan wannan taro da Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Malam Abba Kyari su ka halarta tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnonin da ke kiran a sauke Adams Oshiomhole daga kujerar shugaban jam’iyya su ne: Atiku Bagudu, Nasiru El-Rufai, Simon Lalong, Abubakar Sani Bello da kuma gwamna Godwin Obaseki.

A wani bangare kuma Babagana Zulum, Jide Sanwo-Olu, Gboyega Oyetola, Dapo Abiodun, Abdullahi Ganduje, Aminu Masari, Mala Buni, Yahaya Bello da Abdullahi Sule su na tare da shi.

KU KARANTA: Abin da ya sa Gwamnan Arewa ya yi kaca-kaca da tsohon Gwaman APC

Wasu gwamnoni sun zabi su zama jemagu a cikin wannan rikici da ake yi. Wadannan gwamnoni sun hada da na Jihar Ekiti, Ondo sai Takwarorinsu na Arewa; Gombe, Jigawa, da jihar Kwara.

Rigima ta kaure ne tsakanin wani gwamnan Arewa maso Yamma wanda ya yi kokarin nunawa Takwaransa na wata jihar Arewa ta Gabas, cewa kaunar Buhari ta sa su ke so a tsige Oshiomhole.

Har ta kai Gwamnan na Arewa maso Gabashin kasar ya zargi Abokin aikin na sa da shigowa tafiyar Buhari daga baya. Gwamnan ya yi masa gorin cewa tun 2003 su ke tare da shugaban kasar.

A cewar wannan gwamna, lokacin da su ke fafatukar ganin Buhari ya samu mulki, gudan ya na cikin gungun ‘Yan adawa na jam’iyyar PDP. Buhari ya na ji ya na kallo dai aka yi ta yin wannan.

Shugaban kasar ya ce ya marawa Adams Oshiomhole baya ne saboda aikin da ya yi a NLC da jihar Edo. Buhari ya fadawa manyan jam’iyyar su bi doka idan har za su tsige shugaban na su na kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel